in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a taron koli na masana'antu da kasuwanci a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya
2015-10-22 08:56:29 cri

A yammacin jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na masana'antu da kasuwanci a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya a cibiyar hada-hadar kudi ta birnin London tare da firaministan kasar Birtaniya David Cameron‎.

A jawabin da ya gabatar Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya gudana yadda ya kamata. A cikin yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. Ya ce a don haka za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje domin neman samun bunkasuwa da moriya tare.

Har ila yau Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, ana bukatar sabuwar hanyar neman samun bunkasuwa. A ganinsa, "Shirin ziri daya da hanya daya" zai kawo babban zarafi ga bunkasuwar kasar Sin da kuma kasashen dake kan hanyar siliki.

A nasa bangare, firaministan kasar Birtaniya David Cameron‎ ya bayyana cewa, gwamnatin Birtaniya na dukufa kan raya huldar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin. Ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu ya dace da moriyarsu da ma ta duk duniya. A lokacin da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kawo ziyarar aiki a kasar, bangarorin biyu sun kulla jerin yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa a fannonin makamashin nukiliya da hada-hadar kudi, wanda zai amfana wa jama'ar kasashen biyu sosai.

Ban da haka kuma, Firaminista David Cameron ya ce, gwamnatin Birtaniya ta na maraba da kasar Sin ta zuba jari a wajenta, kuma tana kira ga sassan masana'antu da kasuwanci na kasashen biyu da su kara ba da gundummawa ga huldarsu.

Kafin taron koli, Shugaban na Sin Xi Jinping da Firaministan Birtaniya David Cameron‎ sun shaida bikin kulla yarjejeniyoyi a fannonin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin nukiliya da sauran makamashi da kuma hada-hadar kudi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China