151124-murtala.m4a
|
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da sakon ta'aziyya game da rasuwar dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam'iyyar APC, Prince Abubakar Audu, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
Shugaba Buhari, wanda a yanzu haka yake kasar Iran domin halartar taron kasashe masu arzikin iskar gas, ya bayyana hakan ne ta bakin babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, yana mai cewa babu shakka an yi rashin shugaba mai tausayin al'ummarsa, kuma babban jigo a siyasar Najeriya.
Buhari ya kuma yi fatan Allah yayi wa Abubakar Audu gafara, ya kuma baiwa iyalai da 'yan uwansa, da sauran al'ummar jihar Kogi da ma 'ya'yan jam'iyyar APC da sauran 'yan Najeriya baki daya hakurin jure rashin sa.
Su ma sauran jigajigan jam'iyyar APC, ciki har da shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki, da gwamnan jihar Edo Adams Aliyu Oshiomhole, da sauransu sun bayyana rasuwar Audu a matsayin babban rashi ba ga jihar Kogi kadai, a'a har ma da kasa baki daya. Don haka suka yi fatan Allah ya yi masa gafara.
A jiya Litinin ne aka yi jana'izar Abubakar Audu a garin Ogbonicha na jihar Kogi, jana'izar da ta samu halartar manyan 'yan jami'iyyar APC da dama. (Murtala)