in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan sama na Najeriya sun kai hari kan 'yan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa
2015-11-20 09:35:54 cri
Rundunar mayakan sama ta Najeriya ta yi nasarar lalata makamai da wuraren kerawa da kuma adana makamai na Boko Haram,bayan da ta yi nasarar kaddamar da wasu hare-hare a maboyarsu da ke dajin Sambisa.

Kwamandan rundunar da ke kula da shirin yaki da mayakan Boko Haram mai taken "Lafiya Dole",  Air Kwamado Isiaka Amao shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a garin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Bugu da kari, sojojin sama na Najeriyar sun yi nasarar lalata wasu sansaonin 'yan ta'addan guda biyu da ke dajin na Sambisa, kuma suna ci gaba da luguden wuta ta sama don ganin sun rage karfin 'yan ta'daddan na kai hare-hare kan fararen hula.

Amao ya kuma shaidawa manema labarai cewa, sun samu nasarar kashi 80 cikin 100 a hare-hare sama da 40 da suka kaddamar kan mayakan na Boko Haram a cikin watan Oktoban da ya gabata. Ko da yake sun rasa daya daga cikin matukan jiragensu, amma hakan bai kashe gwiwar sojojin da ke yaki da 'yan Boko Haram din ba.

Har ila yau, sojojin saman sun kame tare da lalata wani kwalale dauke da man fetur da aka yi niyyar kaiwa 'yan ta'addan a kan iyakar Najeriya zuwa Kamaru.

Mayakan na Boko Haram dai na buya a dajin Sambisa ne musamman tsaunukan Gwoza da ke kusa da kan iyakar kasar Kamaru,galibi a lokacin da aka sace mata 'yan makarantar Chibok a watan Afrilun shekarar 2014.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China