in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakrdar MDD ya bukaci dukkan gwamnatoci da su inganta ayyukan taimakon cigaba a hukumance
2015-11-12 13:21:05 cri
Yadda duniya ke kokarin cimma shirin cigaba mai dorewa nan da shekara 2030, Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar laraban nan ya bukaci dukkan gwamnatoci da su inganta ayyukan taimakon cigaba a hukumance.

A yanzu da duniyar ke fuskantar rikici mafi girma na wanda suka rasa matsugunan su tun bayan wanda ya faru lokacin yakin duniya na 2, Mr Ban ya yi kira ga kasashen duniya da su shawo kan wannan kalubale ba tare da yin sanyi a gwiwwa ba inji sanarwar da kakakin majalissar ya fitar ma manema labarai.

Magatakardar ya jaddada muhimmancin da ke akwai na bada gudunmuwar kudi yadda ya kamata na kokarin da ake yi wajen kula da 'yan gudun hijira da masu neman mafaka a kasashen da suka je da kuma ayyukan cigaba mai dorewa.

Kayyakin bukata daga bangare daya bai kamata ya shiga gaban na daya bangaren ba, inji Mr Ban.

Sai dai kuma Magatakardan yayi gargadin cewa rage taimakon a ayyukan cigaba don a dauki nauyin karuwan 'yan gudun hijira zai kara rincabe komai kuma zai jawo mummunan yanayin kamar na kiwon lafiya, ilimi da damammaki na samun rayuwa mai kyau a gida ma miliyoyin al'umma dake kowace kusurwa a duniya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China