Ana fatan dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika wato FOCAC zai tattauna hanyoyin daidaito a kan tattalin arzikin sassan biyu, in ji Jean Bakole, darektan yankin na hukumar raya masana'antu ta MDD wato UNIDO.
A lokacin taron kara wa juna sanin da aka yi a kan filayen masana'antu a Addis Ababa na kasar Habasha, Mr Bakole ya shaida wa Xinhua cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kan cigaban tattalin arzikin Afrika.
Ya ce, Sin ta zama babbar abokiya ta kasashen Afrika da dama, musamman ta bangaren sabbin ayyukan tattalin arziki wadanda suka mai da hankali a kan daga bangaren masana'antu.
Ya yi bayanin cewa, kasar ta Sin ta shiga ayyukan samar da ababen more rayuwa a Afrika na tsawon lokaci, don haka dandalin hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika da za'a yi zai kara ingiza kokarin yadda za'a daidaita hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu domin habaka tattalin arzikin nahiyar baki daya.
Ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasashen Afrika su yi koyi da darussan Sin a fannin masana'antu da ci gaban filayen masana'antun.
A ganin shi, babu wata hanya da kasashen Afrika za su bi su cimma tattalin arziki in ba tare da habaka bangaren masana'antu ba.(Fatimah)