in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FOCAC zai kara samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Afirka, in ji jakadan Sin
2015-11-24 10:37:38 cri

Jakadan kasar Sin a Habasha La Yifan, ya fada a ranar Litinin din nan cewar, dandalin Sin da kasashen Afrika wato FOCAC, wanda ake shirin gudanarwa a farkon wata mai kamawa a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, zai yi matukar tasiri wajen daga likafar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afrika.

A cewar mista La, shugaba Xi na kasar Sin, zai halarci taron domin tattaunawa da shugabannin kasashen na Afrika, don yin nazarin yadda za'a kara karfafa dankon zumuncin dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Jakadan ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, ana sa ran taron zai zakulo hanyoyin da za su kara bunkasa samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Ya kara da cewar, tabbas, babban abin da dandalin zai mayar da hankali a kai, sun hada da batun kasuwanci da zuba jari, da bunkasuwar masana'antu, wadanda su ne manyan hanyoyin dake bunkasa ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Ya ce, batutuwan da za'a duba ba su tsaya iya kasuwanci da zuba jari da masana'antu ba, har ma za'a mayar da hankali kan sha'anin ci gaban ilmi, ta yadda za'a dinga ba da horo domin samar da kyakkyawar makoma ga yara masu tasowa a fadin nahiyar ta Afrika.

Bugu da kari jakadan na kasar Sin ya ce, dandalin zai tabo batun kiwon lafiya, inda kasar Sin da kasashen Afrika za su hada gwiwa domin yakar cututtuka masu saurin yaduwa.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China