in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe: An kaddamar da titin dake hade filin jirgin saman kasar da birnin Harare
2015-11-26 10:41:14 cri
Gabanin ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Zimbabwe, shugaban kasar Robert Mugabe, ya jagoranci bikin kaddamar da wani titin mota da aka fadada, wanda ya hada babban birnin kasar Harare da filin jirgin saman birnin.

An dai maida titin mai tsahon kilomita 12 zuwa tagwayen yanyoyi irin na zamani, aikin da a cewar shugaba Mugabe zai daga martabar kasar a idon masu ziyara, da 'yan kasuwa ko masu zuba jari, da ma masu zuwa yawon shakatawa.

A nasa tsokaci, ministan sufurin kasar Joram Gumbo, cewa yayi bude wannan titi a gabar da shugaba Xi ke daf da gudanar da ziyarar aiki a kasar, wata karramawa ce ga shugaban na Sin. Daga nan sai ya jinjinawa irin tallafin da Sin ke baiwa Zimbabwe, wandanda suka hada da fannin inganta samar da makamashi, da sufuri, da samar da manyan ababen more rayuwa, tare da farfado da tattalin arzikin kasar.

Wasu bayanai daga ofishin jakadancin Sin dake birnin Harare, sun nuna cewa a shekarar 2013, kudaden kasuwancin Sin a Zimbabwe sun kai dalar Amurka miliyan 601, adadin da ya haura na jarin Sin ta zuba a sauran kasashen nahiyar Afirka. Kaza lika a cikin shekaru 3 na baya bayan nan, kudaden lamuni da na rance da Sin ta samarwa Zimbabwe, sun kai dalar Amurka biliyan 1.5.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China