Kwamitin ministoci a Afrika ta Kudu ya fada a ranar Larabar nan cewar, kasar ta shirya tsab domin karbar bakuncin taron shugabannin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika wato FOCAC.
Kwamitin ya ce, tuni an kammala kimtsawa wajen tanade tanaden kayayyakin da ake bukata yayin gudanar da taron, sannan dukkannin tsare tsare da suka hada da na taron manyan jami'ai, da taron ministoci da sauran muhimman al'amurra da suka shafi taron sun kammala.
Kwamitin ya tabbatar da cewar, an kammala shirya wuraren taro a Pretoria da Johannesburg.
Wannan shi ne karon farko da aka daga likafar taron na FOCAC zuwa matsayin taron shugabanni, wanda za'a gudanar tsakanin ranakun 4 zuwa 5 ga watan Disamba. Ana sa ran shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da shugabannin kasashen Afrika da wakilan gwamnatoci za su halarci taron.
Kuma ana sa ran a yayin taron, za'a daddale wani daftari wanda zai tabbatar da hadin kai tsakanin sassan biyu.(Ahmed Fagam)