in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayani kan ziyarar da shugaban kasar zai yi a kasashen Faransa, Zimbabwe, da Afirka ta Kudu
2015-11-26 14:23:17 cri

A ranar Laraba 25 ga watan nan ne aka kira taron manema labaru a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, inda wasu manyan jami'ai suka yi bayani game da ziyarar da shugaban kasar Sin mista Xi Jinping zai yi a kasashen Faransa, Zimbabwe, gami da Afirka ta Kudu.

A wajen taron da aka gudanar a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin dake nan birnin Beijing, mataimakin ministan waje na kasar Sin, mista Liu Zhenmin, ya ce, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Faransa daga ranar 29 zuwa ta 30 ga watan Nuwambar da muke ciki, inda zai halarci bikin bude taron sauyin yanayi na duniya wanda zai gudana a birnin Paris. Hakan a cewar mista Liu ya nuna yadda kasar Sin take dora muhimmanci kan batun sauyin yanayi, kana mataki ne na goyon baya ga kokarin kasar Faransa na karbar bakuncin bikin. Har wa yau a cewar jami'in, a yayin taron shugaban kasar Sin zai bayyana ra'ayin kasarsa kan matakan da ya wajaba a dauka don tinkarar matsalar dumamar yanayin duniya. Kana shugaban zai yi musayar ra'ayi tare da shugabannin wasu kasashe daban daban, game da neman kyautata huldar dake tsakaninsu, gami da sa kaimi ga kokarin cimma matsaya guda a shawarwarin da ake yi don kulla yarjejeniyar Paris.

A na sa bangare, Zhang Ming, wanda shi ma ya kasance mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya yi bayani kan ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Zimbabwe tsakanin ranar 1 zuwa ta 2 ga watan Disamba. A cewar mista Zhang, shugaban kasar Sin zai zanta da takwaransa na kasar Zimbabwe mista Robert Mugabe, sa'an nan za su ganewa idanunsu yadda za a kulla wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2, wadanda za su shafi fannonin aikin gina ababen more rayuwar jama'a, da zuba jari, da fannin raya al'adu, da kiyaye namun daji, da dai sauransu.

Wannan ziyara za ta zama ziyara karo na farko da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Zimbabwe, in ji mista Zhang, wanda hakan ya sa kasar ta Sin ke fatan ganin ziyarar bangarorin 2 za ta bada damar zurfafa zumunci, da kara amincewar juna a fannin siyasa, da tsara matakan hadin gwiwa da za a dauka a nan gaba don kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

Ban da wannan kuma, Zhang Ming ya yi tsokaci kan ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Afirka ta Kudu daga ranar 2 zuwa ta 3 ga watan mai zuwa, ziyarar da ake sa ran za ta haifar da kyakkyawan sakamako, wanda zai kunshi hadin gwiwar da za a gudanar tsakanin bangarorin 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da raya ilimi, da al'adu, gami da kimiyya da fasaha.

Ban da haka kuma, mataimakin ministan ya ce, tun daga ranar 4 zuwa ta 5 ga watan Disamba mai zuwa, shugaban kasar Sin mista Xi Jinping zai yi ziyarara aiki a birnin Johannesberg, don jagorantar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda zai zama wani muhimmin biki, musamman ma a fannonin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka, tare da karfafa hadin gwiwar bangarorin 2.

An ce, a wajen taron ne shugaban kasar Sin zai sanar da wasu muhimman matakan da kasarsa za ta dauka, don taimakawa kokarin kasashen Afirka na raya kai, gami da yaukaka huldar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, ta yadda za a samu damar amfanawa karin jama'ar bangarorin 2.

A cewar mista Zhang Ming, shekarar da muke ciki, ita ce cikon ta 15, tun bayan da aka kaddamar da dandalin tattaunawar hadin gwiwar tsakanin Sin da Afirka. Saboda haka, a taron na wannan karo, za a waiwayi matakan da aka dauka a baya a kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a kara yin amfani da wasu fasahohi masu kyau wajen tsara ayyukan hadin kai da za a gudanar a nan gaba.

Mr. Zhang ya ce akwai abubuwa 2 da ya kamata a mai da hankali a kai dangane da taron, wato da farko taron yana da ma'ana ta musamman a tarihi, wanda hakan ya sa shugabannin kasashen Afirka da na kasar Sin suka taru a waje guda, don nuna wa duniya karfin kasashensu dake kan hanyar tasowa. Sa'an nan na biyu taron zai sa a kara kyautata tsare-tsaren hadin gwiwar bangarorin Sin da Afirka, ta yadda za su kai wani sabon matsayi.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China