in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kociyan U-17 na Najeirya zai ci gaba da jagorantar kungiyar
2015-11-13 10:35:04 cri

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta yanke shawarar baiwa kociyan kungiyar kwallon kafan kasar na 'yan kasa da shekaru 17 Emmanuel Amuneke damar ci gaba da jagorantar kungiyar.

Mataimakin shugaban hukumar na farko Seyi Akinwunmi ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin liyafar da aka shirya don karrama 'yan wasan da suka lashe kofin gasar na 'yan kasa da shekaru 17 na wannan shekara da aka shirya a kasar Chile.

Seyi ya shaidawa mahalarta liyafar cewa, hukumar ta NFF ta amincewa kociyan da ya reni kungiyar zuwa rukunin kungiyar na gaba wato Golden Eaglets, wadda za ta fara shirye-shiryen gasannin cin kofin Afirka da na duniya a shekara mai zuwa.

Bugu da kari, hukumar kwallon kafan kasar ta daga matsayin kociyan zuwa mai taimakawa kociyan 'yan kasa da shekaru 20.

Amuneke dai shi ne ya jagoranci 'yan wasan da suka lashe kofin a karo na biyar, bayan da suka lashe kofin a shekarar 1985, 1993, 2007 da kuma shekarar 2013.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China