A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da madugun jam'iyyar 'yan kwadago ta kasar Birtaniya Jeremy Corbyn a fadar Buckingham.
Mista Xi ya bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Birtaniya a fannin tattalin arziki da cinikayya zai kara karfafa huldar a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Kasar Sin ta jinjinawa gundummawar da jam'iyyar 'yan kwadago ta kasar Birtaniya ta bayar kan huldar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, Jeremy Corbyn ya bayyana cewa, jam'iyyar ta yi maraba da ziyarar Xi Jinping a kasar Birtaniya. Kuma acewar sa kasar Sin ta zama abar misalin a duniya wajen kubutar da mutane miliyan 600 daga kangin talauci. Sannan Birtaniya ta jinjinawa "shirin ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta bullo da shi.(Lami)