in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ronaldo: Ina ganin babu kamar ni
2015-11-05 16:21:18 cri

Ronaldo: Ina ganin babu kamar ni

Shahararren dan wasan gaban kungiyar kwallon kafar Real Madrid wato Cristiano Ronaldo, ya bayyanawa wata mujallar kasar Sifaniya cewa, a ganin sa babu wani dan wasa a duniya da ya kai shi iya murza leda. Kana baya shakka cewa yafi dan wasan Barcelona Leo Messi iya murza tamaula.

Ronaldo wanda ya yi karin haske game da batun takara dake tsakanin sa da Messi, ya ce baya bakin ciki da irin nasarorin da Messin ke samu, illa dai kawai a cewar sa idan aka dubi irin rawar da ya taka cikin shekaru 8 da suka gabata a fagen kwallo, za a yadda cewa shi ne kan gaba a dukkanin fadin wannan duniya.

Game da ihu da magoya bayan Messi suke yi masa kuwa, Ronaldo ya bayyana cewa yana da sha'awar samun abokin takara, domin haka kwallo take, kuma an dade ana yi masa ihu, a cewar kusan tun yana da shekaru 18 ko 19 ake nuna misa adawa. Yace hakan ba matsala ba ce, kara masa kwarin gwiwa ma yake yi.

Daga nan sai ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki zama dan wasa lamba daya a duniya ba. Ya ce dole ne mutum ya yi aiki tukuru, kuma wani lokaci ma akan sha wahalhalu ko raunuka a kokarin tserewa sa'a.

Ronaldo ya ce yana ji a jikin sa, duba da cewa jikin mutum bai cika jure irin wahalhalun da 'yan kwallo ke sha ba, musamman ma lokutan da suka buga wasanni biyu a mako. Duk da hakan dai ya ce yanzu yana kara daukar matakan baiwa jikin sa hutu yadda ya kamata, domin tabbatar da ya ci gaba da kare matsayin bajimtar sa.

Ronaldo ya shidawa wannan jarida cewa kwallo ce rayuwarsa, kuma ita yake burin bugawa a koda yaushe

Real Madrid ta lallasa Las Palmas 3 da 1

Kungiyar Real Madrid ta doke Las Palmas da ci 3 da 1 a wasan La Liga da suka buga a ranar Asabar, inda ta ci gaba da rike matsayin ta na lamba daya a saman teburin gasar, cikin wasannin mako na 10.

Real Madrid din dai ta buga wasannin ta ba tare da manyan 'yan wasan ta irin su Gareth Bale, da Karim Benzema da Sergio Ramos ba, sakamakon jiyya da suke yi. Kaza lika raunin da Keylor Navas ya samu ya baiwa Kiko Casilla damar taka leda a wasan na karshen mako. Real Madrid dai ta gwada kwanjin ta kan Las Palmas, kungiyar da take ta biyu daga kasan teburin gasar.

Isco na Real Madrid ne ya bude ragar Las Palmas, sai kuma kwallon Cristiano Ronaldo mintuna 10 bayan kwallon farko. Mintuna 7 kafin tafiya hutun rabin lokaci ne kuma Hernan ya ramawa Palmas kwallo daya. Kafin akai ga tashi kuma Jese Rodriguez ya kara kwallo ta uku, wadda ta tabbatar wa Madrid din nasarar wasan, aka kuma tashi Real Madrid na da kwallo 3 Palmas na da 1.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China