in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
U17: Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe bayan da ta doke Brazil
2015-11-05 16:22:07 cri

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17, ta doke takwarar ta ta Brazil da ci 3 da nema, a wasan da suka buga a Lahadin karshen makon jiya. Yanzu haka dai Najeriyar ta kai ga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ajin 'yan kasa da shekaru 17 dake wakana a kasar Chile.

Da fari dai Brazil ce ta rike wasan, inda 'yan wasan ta suka rika kai hare-hare ragar Najeriya. Sai dai yanayin wasan ya sauya bayan da dan wasan gaban Najeriya Akpan Udoh ya shigo fili.

A cikin minti na 29 ne kuma Victor Osimhen ya zura kwallo a ragar Brazil. Sai kuma kwallo Kingsley Michael a minti na 30, kafin kuma Udochukwu Anumudo ya zura kwallo ta uku a ragar Brazil.

Dukkanin kokari da 'yan wasan Brazil suka yi na su farke kwallayen ya ci tura, haka kuma aka tashi Najeriya na da kwallo 3 Brazil tana nema. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China