Cikin sanarwar, an ce, shugabannin kasashen da yarjejeniyar RCEP ta shafa suna maraba da sakamakon da aka samu bisa shawarwarin da aka yi, kuma yarjejeniyar na da muhimmiyar ma'ana wajen kyautata zaman rayuwar al'ummomin yankin da kuma raya tattalin arziki, ita ce wata babbar hanya wajen dunkulewar tattalin arziki a wannan yanki. Haka kuma, za ta taimaka ga ciyar da bunkasuwar tattalin arziki cikin adalci, yayin da ake karfafa huldar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa.
Bugu da kari, shguabannin kasashen sun bayyana niyyar sa kaimi wajen karfafa shawarwarin dake tsakanin bangarorin daban daban da abin ya shafa, domin kawo karshensa a shekarar 2016. (Maryam)