Haka kuma gwamantin ta tsayar da kwanaki uku a matsayin na makoki ga wadanda suka rasa rayukansu da suka hada da Sinawa guda 3, Ba'amurke 1 da da Balgian 1.
Jami'an tsaro na kasar sun kaddamar da ayyukan ceto domin su kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a wannan otel din guda 170, yawancinsu 'yan kasashen waje na tsawon awanni 9.
A kalla mutane 27 aka tabbatar da mutuwarsu, sannan an riga an kubutar da saura a cikin otel din na Radison Blu kamar yadda ministan tsaro na kasar Salif Traore ya tabbatar, sa'o'i kadan bayan wannan danyen aikin ta'addanci.
'Yan kasar Sin guda 3 an kashe su ne a gwagwarmayar da aka yi da wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda ofishin jakadancin kasar Sin dake Mali ya tabbatar ma Xinhua a ranar Jumma'a sannan an kubutar da guda 4. (Fataimah Jibril)