in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan kasuwan nan na Nigeriya ya karyata cewa anyi garkuwa da shi a otel din Mali
2015-11-20 20:37:16 cri
Dan kasuwan nan na Nigeriya Alhaji Aliko Dangote ya karyata jita jitan da ake yi cewa yana daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a otel din birnin Bamako na kasar Mali a yau jumma'an nan.

Otel din dai wassu 'yan bindiga suka ma shi zobe a safiyar wannan rana tare da rike mutane 170 da ke ciki a wannan lokacin.

Yace jita jitar cewa yana daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ba gaskiya ba ne. Duk da cewar yana kasar Mali a ranar alhamis, a sakon da ya fitar ta shafin san a twitter.

Kakakin Dan kasuwan Anthony Chiejina tun da farko a cikin wata sanarwa ya yi bayanin cewa ko da yaje Mali, Dan kasuwan bai yi masauki a wannan babban otel din Radisson Blu ba inda harin ya faru.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China