Babbar jami'ar shirin samar da muhalli ta MDD Ana Moreno, ta tabbatar da hakan a hirarta da kamafnin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta ce, ta yi amana cewar babban abin da ke kawo saurin bunkasuwar birane a wannan karni shi ne yadda ake samun ci gaba a nahiyar Afrika da Asiya.
Moreso, ta ce a halin da ake ciki yanzu, sama da rabin al'ummar duniya na rayuwa ne a birane, kuma ana sa ran adadin zai iya karuwa zuwa kashi 70 cikin 100 nan da shekarar 2050.
Ta ce baya ga karuwar yawan al'umma da ake samu a yankunan, har ila yau, ana samun karuwar ci gaban tattalin ariziki da ababen more rayuwa a biranen. Sai dai ta ce, akwai bukatar kasashen su kara kaimi wajen samar da tsare tsare da za su samar da karin ababen more rayuwar domin ya yi daidai da bukatun al'ummar da ke kwarara zuwa biranen.
Moreso ta ce, dole kasashen su samar da wani jadawali na gina biranen domin ya yi daidai da bukatun al'ummar da ke ci gaba da yin tururuwa zuwa biranen.
A cewarta, wata hanya guda da za ta taimaka shi ne ya kamata hukumomin kasashen su yi la'akari da cewar bai kamata su bar birane a makare da al'umma ba tare da samar da wani tsari ba.
Ta ce, akwai bukatar a sake gina matsakaitan garuruwa ta yadda karuwar mutanen ba zai dakile ci gaban manyan birane ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da tsarin kula da muhalli ba.
Ta ce idan har za'a iya samar da tsarin gina matsakaitan garuruwa nan da shekaru 30 masu zuwa, to hakika ba za a fuskanci wata matsala ba ta karuwar kashi 70 na al'ummar da aka yi hasashen samu. (Ahmad Fagam)