Babban hafsan sojin Nigeriya Laftanar Janar Tukur Buratai a ranar Litinin din nan ya ce, sabuwar rundunar da aka kafa a garin Beneshiek dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, musamman an kafa ta ne don a yi yaki da kungiyar Boko Haram.
Janar Burutai ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga sojojin rundunar a garuruwan Beneshiek da Ngamdu.
Ya ce, wadannan wurare suna da muhimmanci, yana mai lura cewa, sabuwar rundunar tana da damar samun nasara a kan kungiyar sosai. Haka kuma yaba sojojin tabbacin cewa, gwamnati za ta samar da dukkan abubuwan da ya kamata da suka hada da kayayyakin aiki don a cimma bukatar da ake da ita ta dakile kungiyar 'yan ta'addan.
Babban hafsan ya kuma ba da tabbaci ga al'umma fararen hula cewa, sojoji za su tabbatar da aiwatar da iyakacin kokarinsu wajen aiki.
A wani bangaren kuma, mataimakin babban sefetan 'yan sandar kasar mai kula da shiyya ta 12 Tunde Ogunsakin ya bukaci 'yan sanda dake karkashin shiyyar jihar Bornon da su kara azama a yakin da ake yi da 'yan kungiyar ta Boko Haram.
Mr Ogunsakin ya bukaci hakan ne a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da ziyararsa a jihar.
Babban jami'in 'yan sanda ya ce, ya je jihar ne don ya kara wa 'yan sandan kwarin gwiwwa, musamman a lokacin da suke ta arangama da 'yan kungiyar ta Boko Haram.(Fatimah)