in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harbi manoma 8 har lahira a Nigeriya
2015-10-29 09:15:44 cri

Manoma guda 8 ne suka rasa rayukansu sanadiyar harbe su da wadansu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi a wani kauye kusa da garin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Nigeriya.

Kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar, an harbi manoman ne a ranar Talata lokacin da suke kokarin tsere wa farmakin 'yan kungiyar ta Boko Haram da suka kai musu hari a kauyen Jakana dake da nisan kilomita 50 daga birnin na Maiduguri.

An yi wa manoman kawanya, sannan 'yan bindigar sun bude musu wuta bayan da suka afka wa kauyen a kan babura. Iyalan mamatan sun yi musu jana'izar a ranar Laraban nan.

Tun da farko dai shugaban Nigeriya Muhammadu Buhari ya riga ya umurni manyan hafsoshin tsaron kasar da su tabbatar da kawo karshen harin 'yan kungiyar nan da karshen wannan shekara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China