in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya na neman 'yan Boko Haram 100
2015-10-29 09:20:31 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ayyana sunayen wasu 'yan Boko Haram su 100 da take nema ruwa a jallo. Rundunar ta ce, tana neman mayakan ne sakamakon zargin da ake yi musu na shiryawa, ko kaddamar da hare-hare a yankunan arewa maso gabashin kasar.

Cikin sunayen wadanda ake neman dai hadda shugaban kungiyar Abubakar Shekau, mutumin da a baya rundunar ta ce, ya riga mu gidan gaskiya. Sauran sun hada da wasu matasa wadanda suka taimaka wajen aiwatar da hare-hare kan al'umma.

Da yake karin haske kan hakan, babban hafsan rundunar sojin kasa laftana Janar Tukur Buratai, ya yi kira ga al'ummar kasar musamman mazauna yankin arewa maso gabas, da su tallafa wa yunkurin sojoji ta hanyar samar da sahihan bayanai, wadanda za su bada damar cafke wadanda ake neman.

Ya kuma kara da cewa, za a fidda layukan tarho na musamman domin baiwa al'umma damar gabatar da sahihan bayanai da ka iya taimakawa hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China