Jami'an tsaro a Najeriya sun cafke guda daga cikin jerin mutane 100 da ake nemansa ruwa a jallo bisa zargin su da nasaba da kungiyar Boko Haram.
Mai magana da yawun rundunar tsaron kasar Kanal Sani Usman, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillacin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Lahadin nan, ya ce a yanzu haka, mutumin mai suna Danladi Abdullahi, yana hannun jami'an tsaro a birnin Maiduguri, helkwatar mulkin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.
Kanal Usman ya ce, ko da yake har yanzu ana tsaka da gudanar da binciken, amma tabbas mutumin sunan sa ne na 26 cikin jerin sunayen da hukumar tsaron ke nema ido rufe, bisa zargin su da alaka da Boko Haram, wanda rundunar sojin kasar ta bazama neman su tun a watan jiya.
Ya ce, tun lokacin da aka fitar da hotunan mutanen 100, hukumomin tsaro da sauran jama'a suka tsananta bincike domin gano 'yayan kungiyar ta Boko Haram.
Daga cikin jerin sunanyen wadanda ake neman, har da jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Mafi yawan wadanda ake neman dai matasa ne da ba su wuce shekaru 29 da haihuwa ba.(Ahmed Fagam)