Hukumomi a Najeriya sun ba da tabbacin sake bude makarantun sakandaren gwamnati a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar a ranar Litinin ta makon gobe tun bayan rufe makarantun sama da shekaru 2 da suka shude.
Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno, shi ne ya tabbatar da haka a yayin ganawa da jakadan kasar Norway Rolf Ree, a ofishin sa dake Maiduguri.
An dai rufe makarantun ne tun a watan Maris na shekarar 2013 a sakamakon hare haren mayakan Boko Haram a jahar Bornon da makwabciyar ta jihar Yobe.
Gwamna Shettima, ya ce, za'a ci gaba da koyarwa a dukkan makarantun sakandaren dake fadin jihar, sai dai za'a takaita koyarwar ne a iya lokutan rana. Ya kara da cewar, nan gaba kadan za'a bude makarantun kwana a fadin jihar.
A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Borno ta fara aiki gina gidaje dubu 2 da 500 ga mutanen da hare haren Boko Haram suka raba da matsugunansu, wadanda a halin yanzu suka fake a makarantun gwamnati a Maiguduri, domin ba da dama ga dalibai su koma azuzuwansu. (Ahmed Fagam)