A tsawon wada'adin aikinmu, a matsayin shugaba na biyu na FOCAC, Afrika ta Kudu za ta cigaba da sanya lura domin ganin cewa ka'adijojin dake tattare da dangantakar dake tsakanin kasashe masu tasowa an girmama su da kuma ganin an bada wata muhimmiyar kulawa ga kokarin tallafi wajen aiwatar da jadawalin shekarar 2063 na tarayyar Afrika (AU), in ji mista Zuma a gaban jakadun kasashen waje da manyan kwamishinoni a yayin wani zaman taro kan manufar siyasar wajen Afrika ta Kudu a birnin Pretoria.
Ajandar shekarar 2063 wani muhimmin shiri ne da nahiyar Afrika ta sanya a gabanta, dake zummar baiwa mata damar gudanar da harkokinsu, da daidaita masana'antu da kuma cigaban tattalin arzikin nahiyar.
A matsayin shugaba ta biyu na FOCAC bisa wa'adin shekarar 2012 zuwa shekarar 2018, Afrika ta Kudu zata karbi dandalin FOCAC karo na biyu a birnin Johannesburg a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba mai zuwa.
Wannan shi ne dandalin FOCAC karo na biyu tun bayan na shekarar 2006, kuma na farko da zai gudana a nahiyar Afrika, inda kuma ake sa ran halartar shugabannin kasashe da gwamnatocin Afrika da dama. (Maman Ada)