Mai Magana da yawun kwamitin na MDD Stephane Dujarric, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis din nan.
A ranar laraba ne dai, yayin da jami'an na UNMISS suka tashi daga babban birnin kasar Juba zuwa yankin Wonduruba, sojojin kwatar 'yancin Sudan wato SPLA suka tsayar da tawagar, sannan suka ci zarafin su har ma an lakadawa wasu daga cikin tawagar duka.
Sakamakon irin mawuyacin halin da jami'an na UNMISS suka fuskanta, ya sa dole suka juya baya suka koma Juba.
Dujarric ya ce, MDD ta yi Allah wadai da wannan al'amari, sannan ta bukaci a gaggauta gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu domin hukunta su.
Kazaika MDD, ta bukaci gwamnatin Sudan ta kudu, ta kyale jami'an na UNMISS da su gudanar da aikin su kamar yadda aka cimma yarjejejniya tun da farko.
An dai kafa UNMISS a ranar 9 ga watan Yulin 2011 ne bayan samun 'yancin Sudan ta kudu, lamarin da ya kawo karshen basasa tsakanin arewaci da kudancin Sudan.
A tsakiyar watan Disambar shekarar 2013 ne dai, rikicin siyasa ya kaure tsakanin shugaban kasar Sudan ta kudun Salva Kiir, da mataimakin sa Riek Machar, lamarin da ya sake jefa kasar cikin wani sabon tashin hankali. (Ahmad Fagam)