in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin kasar Sudan ta Kudu sun musunta labarin da aka bayar wai sun kai hari ga yankin mallakar masu adawa
2015-09-15 10:17:36 cri
A jiya ranar 14 ga wata, kakakin sojojin gwamnatin kasar Sudan ta Kudu Philip Aguer ya musunta labarin da aka bayar wai sojojin sun sabawa yarjejeniyar shimfida zaman lafiya inda suka kai hari ga yankin mallakar masu adawa dake jihar Unity.

Philip Aguer ya bayar da sanarwa cewa, sojojin gwamnatin kasar ba su dauki kowane mataki a jihar Unity ba, sai ma dai dakarun masu adawa ne suka fara kai hari ga sojojin, muradin shi ne son kara kwace yankuna bayan da aka tsagaita bude wuta.

Kungiyar masu adawa ta bayar da sanarwa a ranar lahadi 13 ga wata cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ga sansanonin su biyu a ranar Asabar 12 ga wata, kuma ta yi kira ga kasa da kasa da su yi wa matsin lamba ga gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da ta dauki alhakin wannan hari.

Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta amince da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da kungiyar IGAD ta gabatar a kwanakin baya, daga baya kuma kungiyar masu adawa ta amince da yarjejeniyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China