in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Evergrand, kungiyar wasan kwallon kafa mafi karfi a kasar Sin
2015-11-11 14:55:54 cri

A halin yanzu kasar Sin tana dora muhimmanci ainun a fannin raya harkar wasan kwallon kafa, don cimma burin kasar na kasancewa daya daga cikin kasashe masu karfi a fannin tamaula. Sai dai duk da hakan ba za a iya samun damar cimma wannan buri ba, idan aka gaza samun wasu kuloflikan kwallon kafa masu karfi.

Mun san kasar Sin na da karfin tattalin arziki, wanda hakan ya ba da damar zuba karin kudi a harkar wasan kwallon kafa. Hakan ya taimaka wajen raya kuloflikan wasan kwallon kafa a kasar, gami da gudanar tsarin wasanni mai taken 'Super League', wanda ya kunshi dukkan manyan kuloflika, da 'yan wasa mafiya kwarewa ke taka leda cikin su a kasar ta Sin.

Wadannan kuloflika masu karfi na sassan daban daban na kasar Sin, kamar su Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, amma wanda ya fi karfi a cikinsu duka shi ne kulob din Evergrand dake birnin Guangzhou. A kwanakin baya kungiyar ta lashe kofin gasar 'Super League' na kasar Sin, wanda ya kasance karo na biyar a jere da ta samu wannan nasara.

Ban da gasannin da suke gudana tsakanin kuloflikan kasar Sin, kungiyar Evergrand ita ma ta taka rawar gani a fagen wasan kwallon kafa na duniya. Ga misali, kungiyar ta kasance zakara a gasar da aka gudanar tsakanin manyan kuloflikan nahiyar Asiya a kakar wasa ta 2013. Haka zalika, duk a shekarar ta 2013, kungiyar Evergrand ta zama ta 4 cikin gasar tsakanin kwararrun kuloflikan duniya, wato FIFA Club World Cup a Turance.

Mun san kasar Sin har yanzu ba ta zama wata kasa wadda ta ci gaba a fannin wasan kwallon kafa sosai ba, amma duk da haka kulob din Evergrand ya samu damar raya kansa, har ma ya zamanto daya daga cikin kuloflika masu karfi a duniya. To ko mene ne dalilin da ya sa ya samu wannan nasara?

Dalili na farko kuma mafi muhimmanci shi ne kudi. Mai kulob din Evergrand, kuma wanda ke samar da kudi gare shi wani mutum mai suna Xu Jiayin, wanda ya kasance shugaban wani babban kamfanin gini na kasar Sin. Saboda habakar biranen kasar Sin, yanzu a kasar aikin gini ya kasance wata harkar da aka fi samun riba. Sa'an nan Xu ya yi amfani da kudin da ya samu daga wajen aikin gini don tallafawa kulob dinsa Evergrand, ta yadda kulob din ya samu kwararrun 'yan wasa da yawa.

Tun daga shekarar 2010 har zuwa yanzu, Evergrand ya ware kudi har Euro miliyan 93.1 don shigo da fitattun 'yan wasa daga kasashen waje. Ban da haka kuma, ya samu shahararrun masu horar da 'yan wasa kamar su Marcello Lippi da Luiz Felipe Scolari.

Har ila yau kuma, Evergrand ya yi hadin gwiwa da kulob din Real Madrid wajen kafa makarantar horaswa, ta yadda za a dinga samun kwararrun 'yan wasa matasa a nan gaba. A dayan bangare kuma, kulob din Evergrand ya ware kudi da yawa don hulda da masu sha'awar wasan kwallon kafa. Ya kan ba masu kallon wasan da ya buga kyauta, har ma idan an shiga layin jiran sayen tikitin wasan, sai ya kan samar wa mutane da abinci da shayi. Wannan manufa ta hulda da masu kaunarsa, ta sa kungiyar samun masu goyon baya da yawa, duk a cikin kasar Sin gami da kasashe daban daban na duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China