Kwamitin tsaron yana da nauyin duba ra'ayin dukkan mambobin majalissar da kuma ra'ayin ita kanta MDD, in ji Liu Jieyi wakilin din din din na MDD daga kasar Sin.
A lokacin da yake magana a zauren majalissar ranar Jumma'an nan Mr Liu ya ce kasar Sin ta dade tana goyon bayan kwamitin tsaron a kan kwaskwarimar da yake yi bisa daidaici da sanin ya kamata da nufiin inganta ayyukan shi da kuma ikon shi.
A bisa amincewar babban zauren shawarar mai lamba 62/557 da kuma amincewar yawancin mambobi kasashe, ya kamata a yi shawarwari kan ayyukan kwaskwarima a karkashin jagorancin kasashe mambobi.
Wakilin na kasar Sin ya kuma sanar da cewa, kasar Sin tana fatan wannan tattaunawar za ta bude sabon shafi ta mayar da komai a kan hanyar da ta dace ga mambobi kasashe, a shirya wassu kudurori, a gabatar da shawarwari da kuma kokarin da duk sauran kasashe mambobi suka yi tun lokacin da aka fara shirin yin kwaskwarima a shekara ta 2009. (Fatimah Jibril)