Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhun yana son ci gaba da yin muhawara a fili game da batun hanyoyinsa na gudanar da ayyuka a kowace shekara, da yin alkawarin ci gaba da duba hanyoyin gudanar da ayyuka don kyautata hanyoyin.
Kwamitin sulhun ya yi nuni da cewa, manyan hukumomin MDD musamman kwamitin sulhu, babban taron MDD, hukumar kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma su kara yin mu'amala don kara hadin gwiwa a tsakaninsu da kuma sauran hukumomin shiyya-shiyya.
A shekarun baya baya nan, kwamitin sulhun MDD ya yi muhawara sau da dama kan yadda za a kyautata hanyoyinsa na gudanar da ayyuka. (Zainab)