in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Najeriya ta dakile yunkurin wani mummunan hari a jihar Borno
2015-11-17 09:45:02 cri
Rundunar sojan Najeriya a Litinin din nan, ta samu nasarar dakile wani mummunan hari a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, a yayin da rundunar sojin ta gano sannan ta lalata wata cibiyar harhada boma bomai.

Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriyar a jihar Borno Tukur Ismail Gusau, ya ce an gano wajen harhada boma boman ne a wani wajen dake kusa da garin Bama, kuma daya ne daga cikin yankunan da mayakan Boko Haram ke cin karen su ba babbaka.

An dai samu nasarar tarwatsa sansanin ne tare da tallafin sojojin saman Najeriya, wadanda suka gudanar da bincike ta sama.

Gusau ya kara da cewar, abubuwan da aka gano a yankin, sun hada da wasu sinadarai masu yawan gaske, da wasu kayayyakin ayyukan kimiyya, wadanda ake zaton mayakan Boko Haram ne suka sace a dakunan gwaje gwaje na makarantun yankin Bama kafin a tarwatsa su daga yankin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China