in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta damke wani kwamandan mayakan Boko Haram
2015-11-17 09:17:21 cri
A ranar Litinin din nan jam'ian tsaro a Najeriya, sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin kwamandan kungiyar Boko Haram ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, dake arewa maso gabashin kasar.

Mutumin mai suna John Trankil, an damke shi ne a Kasuwar Shanu dake birnin Maiduguri, mai magana da yawun rundunar sojan Najeriyar Tukur Ismail Gusau ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin.

Kakakin rundunar soja ya ce, bincike na baya bayan nan da suka gudanar ya nuna cewar, kwamandan na Boko Haram da wasu mutane 9 da ake neman su ruwa a jallo suna yawo ne a birnin na Maiduguri, kuma suna yunkurin kaddamar da wani mummunan hari a birnin, ta hanyar amfani da wasu manyan bindigogi da abubuwan fashewa kimanin 20.

A makon da ya gabata, jami'an tsaro a Najeriyar sun samu nasarar damke wasu da dama daga cikin mayakan na Boko Haram wadanda ke cikin jerin sunayen mutane 100 da ake neman ruwa a jallo. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China