Wata sanarwar da rundunar ta fitar ta ce wanda aka cafke mai suna Ishaku Wardifen, daya ne daga mutane 100 da ta dade tana nema. Ya kuma shiga hannu ne a ranar Litinin, a kauyen Maliha dake jihar Adamawa. Sanarwar ta kuma ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa Wardifen dan asalin kasar Kamaru ne.
A ranar Lahadin karshen mako ne jami'an rundunar suka kame Chindo Bello, wanda shi ne na farko da ya shiga hannu, tun bayan fidda sunayen wadanda ake zargin makwanni 3 da suka gabata. An cafke Bello ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake birnin Abuja, a kan hanyar sa ta zuwa birnin jihar Legas. (Saminu Hassan)