Kakakin gwamnatin Chadi ya bayyana cewa, sanarwar dokar ta bacin, na baiwa gwamnan yankin tafkin Chadi damar hana shawagin mutane da ababen hawa a wurare, da takaita lokutan zirga-zirgar jama'a, da kebe yankunan kariya da tsaro, da bada umurnin yin bincike a cikin gidaje da dare ko da rana bisa jagorancin wani babban alkali, domin karbe dukkan nau'o'in kananan makamai dake hannun matune ba bisa ka'ida ba da dai sauransu.
A cewar mista Hassan Sylla Bakari, dokar ta bacin za ta tafiya tare da wasu ayyukan cigaban jama'a, a fannonin da suka shafi noma, kiwon dabbobi, kiwon lafiya da ilimi.
Kakakin ya ce, idan shigar sojojin Chadi a kasashen Kamaru da Najeriya ta taimaka wajen rage karfin kungiyar Boko Haram da kuma ayyukanta, sai dai kuma kasar Chadi ta zama abokar gaba da kaiwa hari ga kungiyar Boko Haram. Ya kuma bayyana cewa tun daga ranar 15 ga watan Yunin shekarar 2015, hare haren kunar bakin wake fiye da biyar ne aka tayar suka janyo tashin hankali a cikin iyalan Chadi. (Maman Ada)