in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram: Sojojin Najeriya sun ceto mutane 20 da aka sace
2015-11-08 12:47:03 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana a ranar Asabar cewa ta ceto mutane 20 daga hannun kungiyar Boko Haram bayan ta kai samame kan sansanoni hudu na kungiyar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Mutanen da kungiyar ta sace, sun hada da kananan yara 14 da mata 6, in ji kanal Tukur Gusau, kakakin rundunar sojojin Najeriya, a Maiduguri, hedkwatar jihar. Haka kuma rundunar ta samar da jinya ga wadannan mutane da ta ceto, in ji kanal Gusau.

Wannan aikin ceto, na cikin tsarin ayyukan da sojojin Najeriya suke kaiwa domin kawar da kungiyar Boko Haram musammun ma a arewa maso gabashin kasar, in ji kanal Gusau.

Wadannan sansanoni hudu an lalata su tare da kashe mayakan kungiyar da dama, in ji ofisan, tare da tabbatar da cewa an kama wasu mutane biyu da ake zaton 'yan ta'adda ne, kuma ana cigaba da yi musu tambayoyi kamar yadda dokokin rundunar sojojin Najeriya suka tanada.

Har ila yau, sojojin sun karbo kayayyaki da dama da mayakan suke amfani da su wajen hada bama bomai a yayin wasu hare-hare da suka kai kusa da kayukan Lagaran Fulani da Ango Baya, in ji kanal Tukur Gusau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China