Alkaluman baya-bayan da asusun na UNICEF ya fitar ya nuna yadda ake samun karuwar mutuwar kananan yara a kasar a watanni biyar na farkon rayuwarsu sakamakon karancin abinci mai gina jiki, inda yara 68 cikin 1,000 ke mutuwa
Mataimakin babban darektan asusun na UNICEF Omar Abdi wanda ya bayyana hakan, bayan ziyarar da ya kai kasar ta Sudan a ranar Lahadi ya ce, yaran na mutuwa ne sakamakon rashin koshin lafiyar mahaifiya da karancin abinci mai gina jiki da kuma matsalolin da matan ke fuskanta a lokacin haihuwa.
Darektan ya ce, hanya guda ta magance cututtukan da ke halaka kaso 6 cikin 100 na yaran ita ce, alluran rigakafi da tsaftace muhalli.
Asusun na UNICEF ya bayyana shirye-shiryen da zai gudanar tare da hadin gwiwar ma'aikatar lafiya ta Sudan don rage yawan yaran da ke mutuwa a kasar. (Ibrahim Yaya)