A wajen kaddamar da wani asusun da aka yi a birnin Landan a wannan makon domin kungiyar kwallon kafar shi ta Yellow Whitsle Blower, ya ce ya zuwa yanzu an tara kusan fan 50,000 kwatankwacin dalar Amurka 76,500 wanda kungiyar Oxfam dake yaki da talauci, da ofishin MDD na 'yan gudun hijira za su yi amfani da shi wajen taimakawa mara sa matsuguni ta hanyar samar masu da abinci, ruwan sha da magunguna.
A hirar da ya yi da kamfanin dillanci labarai na Xinhua, Eto'o ya ce akwai bukatar gwamnatoci, kungiyoyin taimakon jin kai da masu ba da gudunmuwa a ko ina su kara azama a ayyukansu na jinkai domin taimakawa wajen inganta rayuwan wadanda suka rasa matsugunai.
Zaman fargaba da aka yi na shekaru 6 saboda tashin hankalin da kungiyar Boko Haram ta jefa al'umma a ciki a yankunan arewa maso gabashin Nigeriya ya jawo asarar rayuka sama da 1,000 a kasar ta Nigeriya kawai kuma ya bazu zuwa kasashe makwabta kamar su Kamaru, Chadi da jamhuriyar Niger.
A Kamaru kawai an yi kiyasin cewar tsakanin mutane dubu 150-200 dake zaune a yankin arewa mai nisa dake kan iyaka da Nigeriya sun rasa matsugunnan su saboda tashin hankalin kungiyar ta Boko Haram.
A 'yan watannin bayan nan an samu yawaitan harin kunar bakin wake da kungiyar ta rika kai wa wadansu su ma ta hanyar amfani da yara mata kanana. Sojojin Nigeriya dai tare da goyon bayan sojin kasashen Benin, Kamaru, Chadi, Niger sun hada karfi wajen yaki da kungiyar a kokarin kawo karshen ayyukan su. (Fatimah Jibril)