Wang Yi ya yi wannan kira ne yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar G20 da ke gudana a birnin Antalya na kasar Turkiya, bayan hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa da suka yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 132 kana wasu 349 kuma suka jikkata.
Ya ce, kasar Sin ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da aka kai ranar Jumma'a da dare wadanda suka girgiza birnin na Paris, kuma kasar Sin na goyon bayan matakan tsaron da Faransan ke dauka na yaki da ta'addanci.
Mr Wang ya kara da cewa, kamata ya yi a kafa rundunar yaki da ta'addanci, da magance matsalar daga tushe da kaucema yin fuska biyu sannan uwa uba MDD ta kasance a kan gaba a yakin da ake da ayyukan ta'addanci.
Daga karshe, minista Wang ya bukaci kasashen duniya da su sanya batun yakar kungiyar 'yan ta'addan ETIM da ta addabi kasar ta Sin cikin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya.(Ibrahim)