Sin ta yi allawadai da hare haren ta'addancin da aka kai a kasashen Kuwait, Tunisia da Faransa
A jiya Asabar 27 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta bayyana cewa, Sin ta nuna takaicinta sosai kan hare haren ta'addancin da aka kai a kasashen Kuwait, Tunisia da kuma Faransa a ranar Jumma'a 26 ga wata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da yawa suka jikkata. Sin ta nuna ta'aziyarta ga iyalan wadanda suka mutu, tare da jajantawa wadannan kasashe uku, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka ji rauni.
Madam Hua ta kara da cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya riga ya mika sakon nuna alhini ga takwarorinsa na kasashen uku.
Sin ta yi Allah wadai da irin wannan danyen aiki, kuma ta nuna goyon baya ga kokarin kasashen uku na tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa. A sa'i daya, Sin ta bayyana niyyarta ta tinkarar barazanar ta'addanci tare da sauran kasashen duniya baki daya, in ji madam Hua Chunying.(Fatima)