in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 6 suka muta a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci
2015-10-23 18:52:39 cri
Rahotanni daga Maiuduguri babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriya ya tabbatar da cewar an gano gawawwakin mutane 6 safiyar jumma'ar nan da harin kunar bakin wake ya rutsa da su a wata masallaci.

Kamar yadda hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA tayi bayani, harin ya auku ne a wannan masallaci dake unguwar jidari/polo lokacin da jama'a suka shiga sallar asuba.

Majiyar asibitocin yankin sun ce fiye da mutane 17 aka kwantar sakamakon harin da ya rutsa da su.

Fashewar bam din ya rutsa da daya daga cikin wanda ake zargin 'yan kungiyar boko haram ne sauran guda biyu kuma suka tsere lokacin da yan bangar unguwa suka tukaro su bisa zargin da ake na shirya mugun abu, inji wani mazaunin unguwar mai suna Manaseh Adamu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China