in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 27 suka mutu wassu 96 suka jikkata a harin da ya auku a wani masallaci a Nigeriya
2015-10-24 14:04:25 cri
Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewa mutane 27 ne suka mutu sannan wadansu 96 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a garin Yola babban birnin jihar Adamawa.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa na kasar NEMA Sani Datti wanda ya tabbatar da hakan ma Xinhua ta wayar tarho yace wadanda suka jikkatan an kai su asibitin koyarwa na Yola da kuma asibitin kwararru na garin jimeta.

Wannan harin dai ya zo ne kasa da sa'o'i 12 bayan da aka kai wani mummunar harin na kunar bakin wake a wani masallaci dake garin Maiduguri na Jihar Borno duk dai a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai wannan harin ba'a tabbatar da ko mace ce ko namiji ya aiwatar da shi ba inji wani jami'in tsaro dake wajen yana mai bayanin cewa tuni aka killace wajen tare da aiwatar da ayyukan jinkai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China