Yawan mutanen da suka rasu sakamakon harin ranar Litinin da ya gabata, da aka kai unguwar Sabon Gari, dake Jihar Kano a arewacin Najeriya ya karu zuwa 24, baya ga wasu da yanzu haka ke cikin matsanancin halin jinya.
Rahotannin da rundunar hadin gwiwar jami'an tsaron Jihar ta fitar a baya dai sun tabbatar da rasuwar mutane 12 nan take, sakamakon harin da wasu mutane da ba a tatance da su ba suka kaddamar da bindigogi, da kuma ababen fashewa a daren Ranar ta Litinin.
An ce dai harin ya ritsa ne da galibin mutanen dake wannan yanki na Sabon Gari, mai kunshe da mabiya addinin kirista. Da ma dai Jihar ta Kano ta sha fama da hare-hare, daga magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ta fara kaddamar da farmaki a sassan arewacin kasar daban daban tun cikin shekarar 2009.(Saminu)