Shugaban kasar Sin ya gana da shugabannin BRICS
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda a yanzu haka yake birnin Antalya na Turkiya domin halartar taron kolin kungiyar G20 ya gana da shugabannin sauran kasashen kungiyar BRICS. A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya yi kira ga kasashen na BRICS da su karfafa hadin gwiwa da mu'amala da juna, domin yin amfani da damar da suke da ita, da kuma fuskantar kalubale, ta yadda za su samu ci gaba tare.(Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku