Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan a ran 14 ga wata.
Yayin ganawar tasu, Mista Xi ya nuna kyakkyawan fata ga taron koli na G20 da aka bude a birnin Antalya, ya ce, Sin ta darajanta ayyukan da kasar Turkiya ta yi a matsayin kasa dake rike da shugabancin G20. A cewar Mista Xi, Sin za ta dauki bakuncin shirya taron koli na G20 na shekarar 2016, tana fatan kara hadin gwiwa da Turkiya don sa kaimi ga G20 da ta kara taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da kuma ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin daidaici mai dorewa.
Ban da wannan kuma, shugabannin biyu sun yi Allah wadai da harin da aka kai a birnin Paris na Faransa cikin kakkausar murya, kuma sun cimma matsaya daya wajen kara hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta yadda zasu dauki matakan da suka dace wajen yaki da ta'addanci. (Amina)