in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron G20 a kasar Turkiya, inda kuma Xi Jinping zai gabatar da ra'ayoyin kasar Sin
2015-11-15 18:48:11 cri
Taron G20 karo na 10 na manyan kasashen dake da karfin tattalin arziki ya bude a yau Lahadi, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da sauran shugabannin duniya zasu yi kokarin neman hanyoyi da matakan bunkasa cigaban tattalin arzikin duniya.

A yayin wannan taro na kwanaki biyu, Xi zai gabatar da ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin game da yanayin tattalin arzikin duniya, da yin kira da yin hadin gwiwa mafi dorewa domin fuskantar kalubale, da kuma yin aiki tukuru tare da sauran shugabanni domin bullo da wani sabon yunkuri domin bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China