in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan bangarori daban daban za su samu hanyar da ta dace da yanayin kasar Sham domin daidaita batunta
2015-11-13 19:04:12 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Jumma'a cewa, kasar Sin tana fatan bangarori daban daban za su samu hanyar da ta dace da yanayin kasar Sham domin daidaita batun kasar bisa aikin shiga tsakani da MDD take gudana.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya yi bayani kan taron ministocin harkokin waje karo na biyu kan batun Sham da za a shirya a gobe Asabar a birnin Viana, ciki har da wane ne zai shugabantar tawagar kasar Sin, da wadanne sabbin ra'ayoyi ne da kasar Sin za ta gabatar, sannan kuma da sakamakon da kasar Sin ke sa ran a samu a kan wannan taro.

Mr. Hong Lei ya jaddadada cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan wannan taro, sannan mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Li Baodong zai halarci taro a madadin kasar.

Haka kuma, Mr. Hong Lei ya bayyana cewa, bayan da rikicin kasar Sham ya barke, kasar Sin ta gabatar da dabaru game da yadda za'a daidaita batun ba daya ba. Ya ce, "Sin na fatan bangarori daban daban za su nuna sassauci da juna da yi kokarin cimma matsaya daya kan wasu ayyuka domin daidaita batun kasar Sham cikin lokaci"(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China