in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Amurka sun tattauna batun Sham
2015-10-26 12:10:54 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da sanarwa a jiya Lahadi cewa, ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya buga waya ga sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a wannan rana domin ci gaba da tattaunawa kan kokarin kawo karshen rikicin Sham ta hanyar siyasa.

Sanarwar ta ce, ya kamata kasashen dake yankin da abin ya shafa da kuma dukkan kasashen duniya su nuna goyon baya ga daidaita batun kasar Sham ta hanyar siyasa.

A kwanan baya, Sergei Lavrov da John Kerry sun rika tuntubar juna domin tattauna yadda za a daidaita batun kasar Sham. A ranar 23 ga wannan wata, Sergei Lavrov da John Kerry da ministan harkokin waje na kasar Turkey Feridun Sinirlioglu da kuma takwaransa na kasar Saudiyya Adel al-Jubeir sun yi shawarwari a birnin Vienna na kasar Austria, domin tattauna yadda za a gudanar da yunkurin siyasa na daidaita batun kasar Sham. Bangarori 4 da suka halarci taron suna fatan za a yi wani babban taro a ranar 30 ga wannan wata, domin tantance ko ana samun matsaya guda a isashen fannoni don warware batun Sham ta hanyar siyasa. A ranar 24 ga wata kuwa, Sergei Lavrov ya buga waya ga John Kerry, domin ci gaba da tattaunawa kan inganta yunkurin siyasa a tsakanin gwamnatin kasar Sham da wakilan kungiyoyin adawa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China