in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanya daya kawai da za a bi wajen daidaita batun Sham ita ce yin shawarwarin siyasa, a cewar manzon musamman na MDD
2015-10-13 11:13:39 cri

Manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Sham Staffan de Mistura ya jaddada a jiya Lahadi a birnin Geneva cewa, daidaitaciyar hanya daya kawai da za a bi wajen daidaita batun Sham ita ce yin shawarwarin siyasa a tsakanin bangarori daban daban bisa sanarwar Geneva.

Da yake bayanin a taron manema labarai, Staffan de Mistura ya nuna rashin jin dadi game da shawarar da babbar kungiyar adawa ta NCSROF ta kasar ta yanke, game da janye jiki daga halartar shawarwari a tsakanin bangarori daban daban da abin ya ritsa da su ba.

Staffan de Mistura ya ce, zai kai ziyara a kasar Rasha a daren jiya Litinin, daga bisani kuma, zai ziyarci kasar Amurka, a kokarin neman samun karin goyon baya wajen daidaita batun kasar Sham ta hanyar siyasa.

A watan Yuni na shekarar 2012, wakilan kasashen da abin ya shafa ciki har da zaunannun kasashe membobi 5 na kwamitin sulhu na MDD suka bayar da sanarwar Geneva a birnin Geneva, inda suka ba da shawarar kafa gwamnatin wucin gadi da ta kunshi bangarori daban daban, da gyara tsarin mulkin kasar ta hanyar jin ra'ayoyin jama'a, da kuma gudanar da zabe a tsakanin jam'iyyu daban daban.

Saidai a sakamakon sauyawar yanayi a kasar Sham, ba a iya tabbatar da wannan sanarwa ba tukuna .(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China