in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta amsa tambayoyin manema labaru game da taron ministocin harkokin waje kan batun Sham
2015-11-01 17:35:12 cri

A kwanan baya, an yi taron ministocin harkokin waje game da batun Sham a birnin Vienna, inda aka zartas da wata hadaddiyar sanarwa, tare da tsai da wasu manyan ka'idoji kan aikin daidaita batun Sham ta hanyar siyasa.

A game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana a yau Lahadi 1 ga watan Nuwamban cewa, wannan shi ne muhimmin kokari wanda kasashen duniya suke yi wajen daidaita batun Sham yadda ya kamata.

Madam Hua ta kara da cewa, har kullum kasar Sin na himmantuwa wajen ganin an daidaita rikicin Syria a siyasance. "Muna fatan yin kokari tare da kasashen duniya wajen ci gaba da cimma wata mihimmiyar matsaya daya tak domin daidaita batun kasar Sham ta hanyar siyasa."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China