Ma'aikatar tsaron Amurka ta furta a jiya Jumma'a cewar, sojojin kasar za su daina shirin su na horas da kungiyar adawa ta kasar Sham, a maimakon hakan, za su bada goyon bayansu ta wata hanya ta daban domin yaki da kungiyar IS.
Mataimakiyar ministan tsaron Amurka Christine Warmouth ce ta bayyana hakan yayin wani taro. Ta ce yanzu sojojin Amurka sun tsayar da shirin ba da horo ga kungiyar adawa ta kasar Sham sakamakon wasu kalubaloli masu tsanani da suke fuskanta.
Christine, ta kara da cewar, sojojin Amurkan za su samar da jiragen saman yaki da makamai ga dakarun adawa na kasar Sham don amfani da su wajen yaki da kungiyar IS.(Lami)