Kasashen gabashin Afrika za su shirya a birnin Naivasha na kasar Kenya, wani taron tuntubar juna na shiyya kan tasirin El Nino da kuma shirye shiryen ayyukan yin rigakafi a ranar Talata mai zuwa.
Kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD ta jaddada cewa, shirya taron daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Oktoba na da manufar fadakar da kasashe kan illolin El Nino.
Masu shirya taron na fatan yin amfani da dandalin tuntubar juna domin taimakawa kwararrun kasashe da na shiyyoyi wajen fadakar da jama'a da samar da bayanai na baya baya kan El Nino, har ma da shirye shirye a bangaren al'ummomin na dukkan shiyyar, in ji kungiyar IGAD a cikin wata sanarwa a birnin Nairobi.
Taron na tuntubar juna zai taimaka wajen hada masanan yanayi, kwararru a fannin sadarwa, masu fada a ji a fannin siyasa, da ma ministocin kudi, da ministocin dake kula da haduran bala'u na kusurwar Afrika.
Wasu kungiyoyin ba da agaji sun yi gargadin cewa, shiyyar kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara za ta iya fuskantar barazanar yunwa, tare da ruguwar albarkatun noma bisa tasirin El Nino. (Maman Ada)