A cikin wata sanarwar da kakakin majalissar ya fitar, wannan harin da ya auku a ranar Alhamis ya shafi har da jami'an tsaro 'yan kasar ta Irakin dake harabar sansanin.
Mr. Ban baya ga kira da ya yi ma gwamnatin Iraki da ta tabbatar da ta binciki wannan lamari tare da gurfanar da masu laifi gaban shari'a ya kuma jaddada cewa babu dalilin kai irin wadannan hare-hare.
Magatakardar ya tunatar da gwamnatin ta Iraki har ila yau cewa nauyi ne da ya rataya a wuyanta na tabbatar da tsaro ga al'ummar dake wannan sansani.
Haka kuma ya jaddada kudurin majalissar na ci gaba da samar da mafita na taimakon jin kai ga wadanda ke zaune a sansanin na Huriyya tare da yin kira ga gwamnatin na Iraki da masu ruwa da tsaki na sauran kasashen duniya da su gaggauta shirin canza sansanin a matsayin wani mataki na kare lafiyar da samar da karko ma mazauna wajen. (Fatimah Jibril)